عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ سِتٌّ» قِيلَ: مَا هُنَّ يَا رَسُولَ اللهِ؟، قَالَ: «إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ، وَإِذَا دَعَاكَ فَأَجِبْهُ، وَإِذَا اسْتَنْصَحَكَ فَانْصَحْ لَهُ، وَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللهَ فَسَمِّتْهُ، وَإِذَا مَرِضَ فَعُدْهُ وَإِذَا مَاتَ فَاتَّبِعْهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2162]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2162]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi ɗabi'u shida ne: Na farko: Idan ya haɗu da shi ya yi masa sallama da faɗin: Assalamu alaikum, Wato: Aminci ya tabbata agare ku, shi kuma ya dawo da sallama da faɗinsa: Waalaikumus Salam, Wato: Aminci ya tabbata agare ku. Na biyu: Amsa gayyatarsa idan ya gayyace shi dan walima da makamancinta. Na uku: Yi masa nasiha idan ya nemeta, kada ka yi masa yaudara ko ka yi masa algus. Na huɗu: Idan ya yi atishawa sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, to ka gaishe shi da faɗin: (Yarhamukallah) Allah Ya yi maka rahama, shi kuma ya amsa yana mai cewa: Allah Ya shiryar da ku kuma ya gyara zuciyarku. Na biyar: Ya gaishe shi kuma ya ziyarceshi idan ya yi rashin lafiya. Na shida: Ya yi masa sallah idan ya rasu, kuma ya bi jana'izarsa har sai an binne shi.