عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«نِعْمَتَانِ مَغْبُونٌ فِيهِمَا كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ: الصِّحَّةُ وَالفَرَاغُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6412]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6412]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ni'imomi biyu masu girma daga ni'imomin Allah ga mutum wanda da yawa daga mutane suke hasara a cikinsu inda suke juyar da su ba'a mahallinsu ba; domin mutum idan ni'imar lafiya tare da rarar lokaci suka taru gare shi , sai kasala ta rinjaye shi daga ɗa'a to shi yana daga masu hasara; wannan shi ne halin mafi yawancin mutane, idan ya yi anfani da rarar lokaci da kuma lafiyarsa a cikin ɗa'ar Allah to shi mai rabauta ne; inda kuma duniya ita ce gonar lahira, kuma a cikinta akwai kasuwancin da ribarsa take bayyana a lahira, rarar lokaci kuma shagalta tana biye masa, lafiya kuwa rashin lafiya yana biye mata, koda baikasance ba sai tsufa da to ya isa