+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ يَزِيدَ الخَطْمِيِّ قَالَ: حَدَّثَنِي البَرَاءُ وَهُوَ غَيْرُ كَذُوبٍ، قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَالَ: سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، لَمْ يَحْنِ أَحَدٌ مِنَّا ظَهْرَهُ حَتَّى يَقَعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَاجِدًا، ثُمَّ نَقَعُ سُجُودًا بَعْدَهُ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 690]
المزيــد ...

Daga Abdullahi bn Yazid al-Khaɗmi ya ce: Bara'u ya zantar da ni alhali shi ba maƙaryaci ba ne, ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ce: Sami'allahu liman hamidahu (Allah Yaji wanda ya gode maSa) wani ɗaya daga cikinmu baya sunkuyar da bayansa har sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi yana mai sujjada, sai muma mu faɗi muna masu sujjada a bayansa.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 690]

Bayani

Bara'au Dan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari alhali shi mai gaskiyane, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Sami'al lahu liman hamidahu (Allah Yaji wanda ya gode maSa), wanda ke bayansa ba ya gushewa a tsaye, kuma wani ba ya sunkuyar da bayansa dan yin sujjada har sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya goshinsa akan ƙasa, sannan su faɗi suna masu sujjada a bayansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Siffar biyayyar sahabbai ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin sallah, kuma cewa su basa sunkuyawa daga tsayuwa zuwa sujjada har sai ya yi sujjada.
  2. Ibnu Daƙiƙul id ya ce: A cikin haka akwai dalili akan tsawon nutsuwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Akwai halaye huɗu ta ɓangaren koyin mamu tare da limaminsa:
  4. 1- Rigaya: Shi ne ya fara yin abu kafin limamainsa, shi ne mamu ya kai ga rukuni kafin liman ya kai ga wannan rukunin, misali: Ya yi ruku'u kafin liman ya yi ruku'u, ko ya yi sujjada kafin liman ya yi sujjada, to wannan haramun ne, idan ya riga da gangan tare da cewa ya san hakan haramun ne to lallai sallarsa ta ɓaci, daidai ne ya riga shi yin rukuni ne ko kuma ya rigayeshi zuwa rukuni, idan a kabbarar harama ne to sallar sa ma bata ƙullu ba, kuma ya wajaba agare shi ya sake sallah daga farko.
  5. 2- Daidaitawa: Shi ne ya zama ya yi daidai da liman, ya yi ruku'u tare da ruku'unsa kuma ya yi sujjada tare da sujjadarsa kuma ya taso tare da tasowarsa, wannan mafi ƙarancin halayensa ya zama makruhi, amma zahirin dalilai cewa hakan haramun ne, idan ya yi daidai da liman a kabbarar harama to sallarsa bata yi ba kuma waibi ne ya saketa.
  6. 3- Bi: Shi ne ya zo da ayyukan sallah bayan limaminsa ba tare da wani jinkiri ba, wannan shi ne abin da aka shara'anta kuma ya dace da sunnah.
  7. 4- Saɓawa: Shi ne ya saɓawa limaminsa saɓawar da zata iya fitar da shi daga bi, kamar liman ya yi riku'u amma mamu ya tsaya a tsaye har liman ya kusa ɗagowa daga ruku'u, to wannan saɓanin abin da aka shara'anta ne, kuma hakan haramun ne, sai inda wani uzuri, kamar rashin lafiya da kuma tsufa.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin