عَنْ أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَطْعِمُوا الجَائِعَ، وَعُودُوا المَرِيضَ، وَفُكُّوا العَانِيَ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5373]
المزيــد ...
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5373]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi shi ne ya ciyar da mayunwaci, ya ziyarci mara lafiya, ya fanso wanda aka ribace.