عن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قال: رد رسول الله صلى الله عليه وسلم على عثمان بن مظعون التَّبَتُّلَ، ولو أذن له لاختَصَيْنَا.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Sa'ad Dan DanAbiwaqqas-Allah ya yarda- Ya ce: "Annabi-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ya hana Usman Dan Mazoun Kyamar Aure don Ibada kawai, da kuma yai masa Izini da Mun kebanta da sh"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Sa'ad Dan abu Wakkas ya rawaito cewa usman Dan maz'oun sabida tsananin kwadayinsa da Ibada, yayi niyyar kawai ya yanke komai na rayuwa ya kama Ibada, sai ya nemi Iinin Anabi cikin hakan ace ya nisanci Mata kuma ya kama bautar Allah bai yi masa Izinin hakan ba, domin barin dadin rayuwa da kama Ibada kawai, yana daga cikin shishigi a addinikuma wannan Rahabaniyya (Maluntar Kiristoci) wadda Sharia tayi hani da ita, kuma Addini na gaskiya shi ne tsayawa da aikin Allah na Ibada da kuma bawa jiki hakkinsa da jin dadin rayuwa, sabida haka cewa Annabi da yayi Izini ga Usman da dayawa daga cikin masu himmar Ibada sunyi hakan.