عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يَنْظُرُ اللهُ إِلَى رَجُلٍ أَتَى رَجُلًا أَوِ امْرَأَةً فِي دُبُرٍ».
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي في الكبرى] - [السنن الكبرى للنسائي: 8952]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura".
[Ingantacce ne] - - [السنن الكبرى للنسائي - 8952]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana narko mai tsanani da cewa Allah ba Ya duba duban rahama zuwa namijin da ya zo wa namiji ta duburarsa ko mace ta duburarta, kuma hakan laifi ne babba daga cikin manyan laifuka.