+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَلْعُون مَنْ أتَى امرأتَه في دُبُرِها».

[حسن] - [رواه أبو داود والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 2162]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne".

[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 2162]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga miji ya zo wa matarsa ta duburarta; cewa shi tsinanne ne abin korewa daga rahamar Allah, kuma shi babban laifi ne cikin manyan laifuka.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin zakkewa mata ta duburarsu.
  2. Jin daɗi daga mata a koma bayan duburarta na jikinta ya halatta.
  3. Musulmi yana zakkewa mace ne ta farjinta kamar yadda Allah Ya umarce shi; amma ta dubura to a cikin hakan akwai ɓata ɗabi'a, da tozarta zuriya, da saɓawa abinda nagartattun ɗabi'u suke a kansa, da kuma cutuka masu kaiwa ga ma'auratan.