+ -

عَنْ أَبِي بُرْدَةَ الْأَنْصَارِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«لَا يُجْلَدُ أَحَدٌ فَوْقَ عَشَرَةِ أَسْوَاطٍ إِلَّا فِي حَدٍّ مِنْ حُدُودِ اللهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1708]
المزيــد ...

Daga Abu Burda - al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Ba'a yi wa wani mutum bulala sama da goma sai a haddi daga cikin haddodin Allah"

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1708]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi wa wani bulala sama da bulala goma sai dai a cikin saɓo, ba wai ana nufin cewa abinda ya zo a cikinsa na iyakance adadi daga mai shara'antawa na bulala ko duka ko uƙuba keɓantacciya ba, abin nufi ba'a yin ƙari a cikin bulalar ladabtarwa akan bulala goma, kamar yi wa mata bulala ko ɗa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Dokokin Allah - Maɗaukakin sarki - waɗanda Ya yi umarni da su ko kuma ya yi hani daga barinsu suna da uƙubobi waɗanda suke tsawatarwa daga gare su, kodai ababen ƙaddarawa ne daga mai shara'antawa, ko kuma a koma zuwa ga maslahar da shugaba yake ganin ta dace a cikin ƙaddarawarsu.
  2. Ladabtarwa tana kasancewa mai sauƙi gwargwadan fadakarwa da kuma tsoratarwa, saboda haka ba'a ƙari a cikinsa akan bulala goma idan an buƙatu ga hakan, abinda ya fi ladabtar da su ba tare da duka ba, kai da nusarwa, da kuma koyarwa, da shiryarwa, da kwaɗaitarwa, to ya fi sa karɓuwa da kuma sassautawa a cikin koyarwa, halaye a wannan matsayar suna saɓawa da yawa, to yana kamata a aikata abinda ya fi maslaha.