عَنْ أَبِي ثَعْلَبَةَ الخُشَنِيِّ جُرْثُومِ بن نَاشِرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَال:
«إِنَّ اللَّهَ فَرَضَ فَرَائِضَ فَلَا تُضَيِّعُوهَا، وَحَدَّ حُدُودًا فَلَا تَعْتَدُوهَا، وَحَرَّمَ أَشْيَاءَ فَلَا تَنْتَهِكُوهَا، وَسَكَتَ عَنْ أَشْيَاءَ رَحْمَةً لَكُمْ غَيْرَ نِسْيَانٍ فَلَا تَبْحَثُوا عَنْهَا».
[قال النووي: حديث حسن] - [رواه الدارقطني في سننه، وغيره] - [الأربعون النووية: 30]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'alabata alKhushani Jursumu Ibnu Nashir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
[قال النووي: حديث حسن] - [رواه الدارقطني في سننه وغيره] - [الأربعون النووية - 30]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya wajabta wasu abubuwa kuma Ya faralanta wasu farillai, to ku lazimcesu kada ku yi sakaci a cikinsu ta hanyar barinsu ko wulaƙantar da su, kuma Ya sanya muku shamaki da abubuwan da ya tsawatar abubuwan ƙaddarawa waɗanda zasu kareku kuma su tsawatar da ku daga abin da bai yarda da shi ba, dan haka kada ku yi ƙari kan a bin da shari'a ta yi muku umarni da shi, kuma Ya haramta wasu abubuwan da Ya haramta dan haka kada ku aikata su kai karma ku kusancesu, kuma bayan wannan Ya barsu kuma Ya yi shiru game da su dan rahama ga bayinSa, sai suka wanzu akan asalin halaccinsu dan haka kada ku yi bincike game da su.