عَنْ عُمَرَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ لَبِسَ الحَرِيرَ فِي الدُّنْيَا لَمْ يَلْبَسْهُ فِي الآخِرَةِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5834]
المزيــد ...
Daga Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya sanya alhariri a duniya ba zai sanya shi a lahira ba"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5834]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya sanya alhariri cikin maza a nan duniya ba zai sanya shi a lahira ba idan bai tubaba dan ukuba gare shi.