عَن عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ أَبِي لَيْلَى أَنَّهُمْ كَانُوا عِنْدَ حُذَيْفَةَ، فَاسْتَسْقَى فَسَقَاهُ مَجُوسِيٌّ، فَلَمَّا وَضَعَ القَدَحَ فِي يَدِهِ رَمَاهُ بِهِ، وَقَالَ: لَوْلاَ أَنِّي نَهَيْتُهُ غَيْرَ مَرَّةٍ وَلاَ مَرَّتَيْنِ -كَأَنَّهُ يَقُولُ: لَمْ أَفْعَلْ هَذَا-، وَلَكِنِّي سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«لاَ تَلْبَسُوا الحَرِيرَ وَلاَ الدِّيبَاجَ، وَلاَ تَشْرَبُوا فِي آنِيَةِ الذَّهَبِ وَالفِضَّةِ، وَلاَ تَأْكُلُوا فِي صِحَافِهَا، فَإِنَّهَا لَهُمْ فِي الدُّنْيَا وَلَنَا فِي الآخِرَةِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5426]
المزيــد ...
Daga AbdurRahman Dan Abu Laila cewa sun kasance a wajen Huzaifa, sai ya nemi a shayar, sai wani Bamajushe ya shayar da shi, lokacin da ya ajiye ƙwaryar a hannunsa sai ya jefe shi da ita, kuma ya ce: Da badan ni na hana shi ba, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba - kamar cewa shi ya ce: Ban aikata wannan ba -, sai dai cewa ni na ji annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5426]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana maza sanya alhariri da dukkan nau'o'insa. Kuma ya hana maza da mata ci da sha a kofinan zinari da azirfa. Kuma ya bada labari cewa su na muminai ne a ranar lahira; domin su sun nisancesu a duniya dan biyayya ga Allah, Amma kafirai to ba su da rabonsu a lahira; domin su sun yi gaggawar daɗaɗasu a rayuwarsu ta duniya dan sun riƙesu, da kuma saɓawarsu ga umarnin Allah.