+ -

عَنْ رَافِعِ بْنِ خَدِيجٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِذِي الحُلَيْفَةِ، فَأَصَابَ النَّاسَ جُوعٌ، فَأَصَابُوا إِبِلًا وَغَنَمًا، قَالَ: وَكَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي أُخْرَيَاتِ القَوْمِ، فَعَجِلُوا، وَذَبَحُوا، وَنَصَبُوا القُدُورَ، فَأَمَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِالقُدُورِ، فَأُكْفِئَتْ، ثُمَّ قَسَمَ، فَعَدَلَ عَشَرَةً مِنَ الغَنَمِ بِبَعِيرٍ فَنَدَّ مِنْهَا بَعِيرٌ، فَطَلَبُوهُ، فَأَعْيَاهُمْ وَكَانَ فِي القَوْمِ خَيْلٌ يَسِيرَةٌ، فَأَهْوَى رَجُلٌ مِنْهُمْ بِسَهْمٍ، فَحَبَسَهُ اللَّهُ، ثُمَّ قَالَ: «إِنَّ لِهَذِهِ البَهَائِمِ أَوَابِدَ كَأَوَابِدِ الوَحْشِ، فَمَا غَلَبَكُمْ مِنْهَا فَاصْنَعُوا بِهِ هَكَذَا»، فَقَالَ أي رافع: إِنَّا نَرْجُو -أَوْ نَخَافُ- العَدُوَّ غَدًا، وَلَيْسَتْ مَعَنَا مُدًى، أَفَنَذْبَحُ بِالقَصَبِ؟ قَالَ: «مَا أَنْهَرَ الدَّمَ، وَذُكِرَ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ فَكُلُوهُ، لَيْسَ السِّنَّ وَالظُّفُرَ، وَسَأُحَدِّثُكُمْ عَنْ ذَلِكَ: أَمَّا السِّنُّ فَعَظْمٌ، وَأَمَّا الظُّفُرُ فَمُدَى الحَبَشَةِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2488]
المزيــد ...

Daga rafi'u ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, sai suka samu raƙuma da tumakai, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikin ƙarshen mutane, sai suka yi gaggawa, suka yanka, suka girka tukwane, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da tukwane, sai aka kifar da su, sannan ya raba, sai ya daidaita tumakai goma da raƙumi ɗaya sai wani raƙumi ya yi tsaurin kai, sai suka neme shi, sai ya gajiyar da su kuma a cikin mutanen dawakan kaɗan ne, sai wani mutum daga cikinsu ya sunkuyar da kibiya, sai Allah Ya tsare shi, sannan ya ce: "Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'. Sai ya ce: wato rafi'u: Lallai mu muna jin kwadayi - ko muna jin tsron - makiya gobe, kuma babu wuka a tare da mu, shin zamu yanka ne da kara? ya ce: "Duk abinda ya zubar da jini, kuma aka ambaci sunan Allah akansa to sai ku ci shi, banda hakori da farce, kuma zan zantar da ku game da haka: Amma a hakori to kashi ne, amma farce to wuƙar mutanen Habasha ce".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2488]

Bayani

Rafi'i ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-Hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, alhali sun samu ganimar raƙuma da tumakai daga mushrikai, sai suka yi gaggawa kafin raba ganima sai suka yanka wasu daga cikinsu, kuma suka kafa tukwane, ba tare da sun nemi izinin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba, kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a cikin ƙarshen mutane, lokacin da (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sani sai ya yi umarni da tukwanan, sai aka kifar da su da abinda ke cikinsu na miya, sannan ya raba ganimar a tsakaninsu, sai ya sanya goma daga cikin tumakai a madadin rakumi daya, sai wani rakumi ya gudu daga cikinsu, sai suka kasa kama shi, kuma dawakan sun kasance kada ne, sai wani mutum ya harbe shi da kibiya, sai Allah Ya tsare musu shi, sai (Annab) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai akwai wasu ɗabi'u kamar ɗabi'un daji ga waɗannan dabbobin masu sabo, wanda ya rinjayeku daga cikinsu kuma kuka kasa kama shi to ku yi haka da shi. Sai Rafi'u ya ce: Lallai mu mana fatan fuskantar maƙiya gobe, kuma muna jin tsoron yankanmu ga dabbobin ya cutar da makamanmu alhali ana tsananin buƙatar yanka, kuma babu wuƙa a tare da mu, shin zamu yanka ne da busassun karare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk abinda ya zubar da jini kuma ya kwaranyar da shi da yawa, kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to ku ci shi, banda haƙori da farce, kuma zan zantar daku game da hakan: Amma haƙori to ƙashi ne, amma farce to mutanen Habsha kafirai ne suke amfani da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayyanar da wani ɓangare daga tawali'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tafiyarsa a bayan runduna, da kuma kula da sahabbansa, da bibiyarsa garesu, da karɓar nasihar sahabbansa - Allah Ya yarda da su -.
  2. Ladabatarwar shugaba ga talakawansa da kuma rundunarsa, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ladabtar da su akan wannan gaggawar da kuma aikin da suka yi, kafin karɓar izninsa, sai sakamakonsu ya zama haramta musu abinda suka yi nufi.
  3. Gaggawar amsawar sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare su -.
  4. Hana ɗaukar ganima har sai an rabata.
  5. Adalci, musammanma agurin yaƙar maƙiya da kafirai; domin hakan yana daga sabubban nasara da rinjaye akan maƙiya.
  6. Nawawi ya ce: Idan dabbar gida ta koma mai ɗabi'ar ta daji shi ne raƙumi ko saniya ko doki su yi taurin kai ko akuya ta gudu ko waninsu to shi ya zama kamar farauta ne, sai ya halatta ta hanyar harbi.
  7. Yankan dabbobi yana wajaba dan cinsa ya halatta, dabbobi an sharɗanta musu abinda ke tafe:
  8. 1- Ya zama cinsa ya halatta.
  9. 2- Ya zama an samu iko a kansa, wanda ba'a samu iko a kansa ba to hukuncinsa shi ne hukuncin abin farauta.
  10. 3- Ya zama dabba ce ta sarari; amma dabbar ruwa to ba'a sharɗanta yanka gareta ba.
  11. Sharuɗɗan ingancin yanka:
  12. 1-Cancantar mai yankan shi ne ya zama mai hankali mai mayyazewa kuma musulmi ko mazuwa littafi (Bayahude ko Banasare).
  13. 2- Ya ambaci sunan Allah a farkon yankan.
  14. 3- Ingancin abin yankan ga yanka shi ne abin yankan da za’a yi amfani da shi ya zama mai kaifi cikin kowane irin abu ne banda haƙori da farce.
  15. 4- Yankan ya zama gurin da ake yankawane ko kuma sokewa a abinda ake da iko akansa ta hanyar yanke maɗaciya da maƙogwaro da jijiyoyi.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin