lis din Hadisai

"Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu*, idan za ku yi kisa, to, ku kyautata kisan, kuma idan za ku yi yanka, to, ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa, ya hutar da abin yankansa".
عربي Turanci urdu
Na jewa Manzon Allah SAW sai na ce ya Manzon Allah mu muna kasar da Ahlil kitabi bi shin zamu iya cin abunci a Koransu ?
عربي Turanci urdu
An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta
عربي Turanci urdu
Ida Quda ya faxa cikin abun shan xayanku to ya dulmuya shi sannan sai ya cire shi; saboda a cikin xayan fuka fukansa akwai cuta a xayan kuma Maganinta
عربي Turanci urdu
"Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".
عربي Turanci urdu
"Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne".
عربي Turanci Indonisiyanci
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
عربي Turanci urdu
Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza
عربي Turanci urdu
Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, sai suka samu raƙuma da tumakai, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikin ƙarshen mutane, sai suka yi gaggawa, suka yanka, suka girka tukwane, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da tukwane, sai aka kifar da su, sannan ya raba, sai ya daidaita tumakai goma da raƙumi ɗaya sai wani raƙumi ya yi tsaurin kai, sai suka neme shi, sai ya gajiyar da su kuma a cikin mutanen dawakan kaɗan ne, sai wani mutum daga cikinsu ya sunkuyar da kibiya, sai Allah Ya tsare shi, sannan ya ce: @"Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'*. Sai ya ce: wato rafi'u: Lallai mu muna jin kwadayi - ko muna jin tsron - makiya gobe, kuma babu wuka a tare da mu, shin zamu yanka ne da kara? ya ce: "Duk abinda ya zubar da jini, kuma aka ambaci sunan Allah akansa to sai ku ci shi, banda hakori da farce, kuma zan zantar da ku game da haka: Amma a hakori to kashi ne, amma farce to wuƙar mutanen Habasha ce".
عربي Turanci urdu
Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce ni da in tsaya a jikinsa, kuma in yi sadaka da namansu da fatarsu da kuma lokacinsu
عربي Turanci urdu
"Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka"*, sai aka ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin kitsen mushe, cewa su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma ana shafe fatu da su, kuma mutane suna fitila da su? sai ya ce: "A'a, shi haramun ne", sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a wannan lokacin: "Allah Ya la'anci Yahudawa lallai Allah yayin da Ya haramta kitsensu sai suka gyara shi, sannan suka saida shi, sai suka ci kuɗinsa".
عربي Turanci urdu
Idan ka aika karanka na farauta kuma ka ambaci sunan Allah, to abinda duk abinda ya kamo maka
عربي Turanci urdu
"Aan tambay Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi-game da giya da ake daukanta a matsayin tsumi? sai ya ce: A'a"
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Umarni da a Kashe Tsaka kuma ya ce: ta kasance tana busa ga Annabi ibrahim
عربي Turanci urdu
Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye.
عربي Turanci urdu
Mun ta so Zomo a kwarin Zahran sai Mutane suka bishi a guje sai suka ka kasa
عربي Turanci urdu
Munyi yaki tare da Manzon Allah Yakuna guda bakwai, muna ta cin Fara
عربي Turanci urdu
"Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana"*, Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.
عربي Turanci urdu
Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: @Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata*, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.
عربي Turanci Indonisiyanci