+ -

عن عديّ بن حاتم رضي الله عنه قال: قلتُ: يا رسول الله، إني أُرسلُ الكلاب المعلَّمة، فيُمسِكنَ عليّ، وأذكرُ اسم الله؟ فقال: "إذا أرسلتَ كلبَكَ المعلَّمَ، وذكرتَ اسمَ الله، فكُلْ ما أمسكَ عليك"، قلت: وإن قتلنَ؟ قال: "وإن قَتلْنَ، ما لم يَشْرَكْها كلبٌ ليس منها"، قلتُ له: فإني أرمي بالمِعْراض الصيدَ فأُصُيبُ؟ فقال: "إذا رميتَ بالمعراضِ فخزَقَ فكلْهُ، وإن أصابَه بعَرْضٍ فلا تأكلْهُ". وحديث الشعبي، عن عدي نحوه، وفيه: "إلا أن يأكل الكلب، فإن أكل فلا تأكل؛ فإني أخاف أن يكون إنما أمسك على نفسه، وإن خالطها كلاب من غيرها فلا تأكل؛ فإنما سميت على كلبك، ولم تسم على غيره". وفيه: "إذا أرسلت كلبك المكلب فاذكر اسم الله، فإن أمسك عليك فأدركته حيا فاذبحه، وإن أدركته قد قتل ولم يأكل منه فكله، فإنَّ أخْذَ الكلبِ ذَكَاته". وفيه أيضا: "إذا رميت بسهمك فاذكر اسم الله". وفيه: "فإن غاب عنك يوما أو يومين -وفي رواية: اليومين والثلاثة- فلم تجد فيه إلا أثر سهمك، فكل إن شئت، فإن وجدته غريقا في الماء فلا تأكل؛ فإنك لا تدري الماء قتله، أو سهمك؟
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Adiyyu Dan Hatim ya ce nace: Ya manzon Allah ni ina cuna kare na na farauta, sai ya kamo mun farauta, kuma in ambaton sunan Allah ? sai ya ce: "Idan ka aika karanka na farauta kuma ka ambaci sunan Allah, to abinda duk abinda ya kamo maka" sai nace to idan ya kashe fa? sai ya ce: "kuma koda sun kashe indai ba wani karen ne ya taya shi ba" sai nace da shi: to ni wani lokaci ina jifansa da Mashi kuma in same shi? sai ya ce idan ka jefeshi idan ya same shi da tsinin to kaci in kuma da gorar ne kada kaci, kuma a Hadisin Sha'abi daaga Adiyyu kwatankwacinsa a cikinsa: "sai dai idan karen yaci, idan yaci kada kaci; domin ina tsoron ko yakamawa kansa ne, kuma idan wani karen ya tayata kada kai, domin Bisimillarka ta karenka ce, bakayi akan waninsa ba" kuma a cikin wani Hadisin: "Idan ka aika karanka na farauta kuma ka ambaci sunan Allah, to abinda duk abinda ya kamo maka" acikin wani kuma: "Idan ka jefa kibiyarka to ka ambaci Allah" kuma a cikinsa: "kuma idan ya bace maka kwana daya ko biyu-kuma a cikin wata Riwayar: kwana biyu ko uku- baka samu komai a jikinsa ba sai miki kibiyarka, to kaci idan kaga dama, idan kuma kaganshi ya nitse a ruwa kada kaci; domin baka sani ba ruwa ne ya kashe ba ko mashinka"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Adiyyu Dan Hatim ya tambayi Annabi dangane da farauta da karnukan farauta, kuma wanda mai shi ya koyar da shi, sai ya ce: kuma duk abinda suka kama maka idan dai ka ambai Allah akansa matukar dai baka samu wani karen tare da shi ba, idan ka sami wani karen tare da shi to kada ka ci domin kai ka yi bisimillah ne akan karenka kawai bakayi a daya karen ba, haka idan kai jifa da Mashi sai ya soki dabbar kuma jini ya futa duk wannan sabida yin Bisimillah, kuma idan gorar ce ta same shi ba tsini ba to kada ka ci, domin ya Mutu da bigewa ne sai ya zamo kamar wanda ya gangaro daga sama ko aka tunkuye shi, kuma idan ya cuna karensa kuma ya same shi da ransa to ya wajaba ya ranka shi a lokacin kuma ya zamanto halak ne kuma koda tare da wani karen suka kama, kuma ya tambaye shi game da farautar dabba da jifa da Mashi idan aka ambaci sunan Allah, sai ya Umarce shi daya ci kuma idan ya gudu ya kai kwana daya ko biyu kuma da yaganshi babu komai a jikinsa sa tabon Mashinka to ya halatta yaci kuma idan ya same shi ya nutse a ruwa to kada ya ci domin bai san mai ya kashe shi ba Mashinka ne ko kuma ruwan ne?

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin