عن أبي بشير الأنصاري رضي الله عنه "أنه كان مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في بعض أسفاره، فأرسل رسولا أن لا يَبْقَيَنَّ في رقبة بَعِيرٍ قِلادَةٌ من وَتَرٍ (أو قلادة) إلا قطعت".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin sashin tafiye tafiyansa ya aiki wani jakada a bisa cewa kada ya bar wata laya ko rataye a wuyan wani rakumi face ya tsinke ta
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Lallai cewa Manzon Allah SAW ya aika a cikin wata tafiyarsa wanda zai shela cikin Mutane da kowa ya cire layun da suke wuyan Rakuma wanda aka saka su don maganin kanbun baka, da kawar da rashin lafiya; saboda haka yana daga cikin Shirka wacce ya wajaba a kawar da ita.