+ -

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ الْجُهَنِيِّ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقْبَلَ إِلَيْهِ رَهْطٌ، فَبَايَعَ تِسْعَةً وَأَمْسَكَ عَنْ وَاحِدٍ، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، بَايَعْتَ تِسْعَةً وَتَرَكْتَ هَذَا؟ قَالَ: «إِنَّ عَلَيْهِ تَمِيمَةً»، فَأَدْخَلَ يَدَهُ فَقَطَعَهَا، فَبَايَعَهُ، وَقَالَ: «مَنْ عَلَّقَ تَمِيمَةً فَقَدْ أَشْرَكَ».

[حسن] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 17422]
المزيــد ...

Daga Uƙuba ɗan Amir Aljuhani - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane sun fuskanto gare shi , sai ya yi wa tara daga cikinsu caffa (Mubaya’a) yaki yi wa ɗaya, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka yi wa tara caffa ka bar wannan? ya ce: "Atare da shi akwai laya". Sai ya shigar da hannunsa sai ya yanketa, sai ya yi masa caffa, ya ce: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

[Hasan ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 17422]

Bayani

Wasu jama'a sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, adadinsu su goma ne, sai ya yi Mubaya’awa tara daga cikinsu (Wato caffa) akan Musulunci da bi, bai yi wa na goman ba, yayin da aka tambaye shi game da sababin hakan sai tsira da amincin su tabbata agare shi ya ce: Lallai atare da shi akwai laya, ita ce abinda ake ɗaurawa ko ake ratayawa na laya (guru ko kamun) ko waninsa don tunkuɗe kanbun baka ko wata cuta. Sai mutumin ya shigar da hannunsa gurin layar ya yanketa ya kuɓuta daga gareta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa caffa, ya ce yana mai gargaɗarwa daga layu yana mai bayyana hukuncinsu: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wanda ya dogara ga wanin Allah, Allah Zai yi masa mu'amala da saɓanin nufinsa.
  2. Kudirce cewa rataya layu sababi ne na tunkuɗe cuta da kanbun baka to ƙaramar shirka ce, amma idan ya ƙudirce cewa suna amfanarwa da kansu to hakan babbar shirka ce.