+ -

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا أَسْكَرَ كَثِيرُهُ فَقَلِيلُهُ حَرَامٌ».

[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 3681]
المزيــد ...

Daga Jabir ɗan Abbdullahi - Allah Ya ƙara yarda a gare su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne".

[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 3681]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abin sha ko abin ci da yake kawar da hankali lokacin da aka ci ko aka sha mai yawa daga gare shi, to cin kaɗan daga gare shi abin haramtawa ne koda bai tafiyar da hankali ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kiyayewar shari'a akan hankulan mutane.
  2. Ingancin lura da toshe kafa, hakan ta hanyar kulle dukkan abinda yake kaiwa zuwa waɗannan munanan abubuwan.
  3. Haramta kaɗan na abinda yake sa maye; domin shi tsani ne ga maye.
  4. idan kaɗan ɗinsa ko mai yawansa baisa maye ba, to shi ba haramun ba ne.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin