+ -

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«كل مُسْكِرٍ خَمْرٌ، وكل مُسْكِرٍ حرام، ومن شرِب الخمر في الدنيا فمات وهو يُدْمِنُهَا لَمْ يَتُبْ، لَمْ يَشْرَبْهَا في الآخرة».

[صحيح] - [رواه مسلم وأخرج البخاري الجملة الأخيرة منه] - [صحيح مسلم: 2003]
المزيــد ...

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".

[Ingantacce ne] - - [صحيح مسلم - 2003]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
  2. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
  3. Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
  4. Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
  5. Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.