عن أنس رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«جَاهِدُوا المشركين بأموالكم وأنفسكم وألسنتكم».
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وأحمد] - [سنن أبي داود: 2504]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 2504]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan:
Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan.
Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu.
Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.