عَنْ مُعَاذٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا وَجَّهَهُ إِلَى الْيَمَنِ أَمَرَهُ أَنْ يَأْخُذَ مِنَ الْبَقَرِ مِنْ كُلِّ ثَلَاثِينَ تَبِيعًا أَوْ تَبِيعَةً، وَمِنْ كُلِّ أَرْبَعِينَ مُسِنَّةً، وَمِنْ كُلِّ حَالِمٍ -يَعْنِي مُحْتَلِمًا- دِينَارًا أَوْ عَدْلَهُ مِنَ المَعَافِرِ، ثِيَابٌ تَكُونُ بِالْيَمَنِ.
[صحيح بشواهده] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 1576]
المزيــد ...
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi -:
Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin, haka (ya karɓi) Musinnah daga dukkanin (shanu) arba'in, daga (ya karɓi) dinari ɗaya ko kwatankwacinsa na Ma'afir wasu tufa ne na Yaman daga duk wanda ya isa mafarki.
[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa] - - [سنن أبي داود - 1576]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - zuwa Yaman dan koyar da mutane da kuma kiransu, daga cikin abin da ya umarce shi da shi shine ya karɓi Zakkar shanunsu tabi'i ɗaya namiji ko mace daga dukkanin talatin; shine wanda ya cika shekara ɗaya, haka (ya karɓi) Musinna daga dukkanin arba'in; ita ce wacce ta cika shekara biyu. Kuma ya karɓi jizyar dinari ɗaya daga mazowa littafi Yahudawa da Nasara daga dukkanin namiji baligi, ko abin da ya yi daidai da dinari ɗaya na tufafin Yaman waɗanda ake kiransu da: Ma'afirri.