+ -

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ قَتَلَ مُعَاهَدًا ‌لَمْ ‌يَرَحْ ‌رَائِحَةَ الْجَنَّةِ، وَإِنَّ رِيحَهَا تُوجَدُ مِنْ مَسِيرَةِ أَرْبَعِينَ عَامًا».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 3166]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3166]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin kashe kafirin amana da zimmi da musta'aman (wanda aka ba shi amincin ɗan wani lokaci) daga kafirai, kuma cewa hakan babban laifi ne daga manyan laifuka.
  2. Kafirin amana: Shi ne wanda aka yi alƙawari da shi daga kafirai a kan ya zauna a garinsa ba zai yaƙi musulamai ba su ma ba za su yaƙe shi ba. Zimmi kuma: Shi ne wanda ya zauna a garin musulmai ya ba da jizya. Musta'aman kuma: Shi ne wanda ya shiga garin musulmai a kan alkawari da aminci na wani ƙayyadajjen lokaci.
  3. Gargaɗi daga ha'intar alƙawurra (da aka ƙulla) tare da wanin musulmai.