عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
وُقِّتَ لَنَا فِي قَصِّ الشَّارِبِ، وَتَقْلِيمِ الْأَظْفَارِ، وَنَتْفِ الْإِبِطِ، وَحَلْقِ الْعَانَةِ، أَلَّا نَتْرُكَ أَكْثَرَ مِنْ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 258]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, kada mu bari sama da dare arba'in.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 258]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance akan rage gashin bakin namiji, da yanke farcen hannaye da ƙafafuwa, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, cewa kada a barsu sama da kwanaki arba'in.