عَنْ أَبِي بُرْدَةَ، عَنْ أَبِيهِ أَبِي مُوسَى الأَشْعَريِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَعَثَهُ إِلَى اليَمَنِ، فَسَأَلَهُ عَنْ أَشْرِبَةٍ تُصْنَعُ بِهَا، فَقَالَ: وَمَا هِيَ؟، قَالَ: «البِتْعُ وَالمِزْرُ»، فَقِيلَ لِأَبِي بُرْدَةَ: مَا البِتْعُ؟ قَالَ: نَبِيذُ العَسَلِ، وَالمِزْرُ: نَبِيذُ الشَّعِيرِ، فَقَالَ: «كُلُّ مُسْكِرٍ حَرَامٌ» خرجه البخاري.
وَخَرَّجَهُ مُسْلِمٌ وَلَفْظُهُ: قَالَ: بَعَثَنِي رَسُولُ اَلله أَنَا وَمُعَاذٌ إِلَى اَليَمَنِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولُ اَللَّهِ! إِنَّ شَرَابًا يُصْنَعُ بِأَرْضِنَا يُقَال لَهُ: المِزَرُ مِنَ الشَّعِيرِ، وَشَرَابٌ يُقَالُ لَهُ: البِتْعُ مِنَ العَسَلِ، فَقَالَ: «كُلُّ مُسْكِرٍ حَرَامٌ».
وَفِي رِوَايَةٍ لِمُسْلِمٍ: «فَقَالَ: كُلُّ مَا أَسْكَرَ عَنِ الصَّلَاةِ فَهُوَ حَرَامٌ».
وَفِي رِوَايَةٍ لَهُ: «وَكَانَ رَسُولُ الله قَدْ أُعْطِيَ جَوَامِعَ الكَلِمِ بِخَوَاتِمِهِ، فَقَالَ: أَنْهَى عَنْ كُلِّ مُسْكِرٍ أَسْكَرَ عَنْ الصَّلَاةِ».
[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 46]
المزيــد ...
Dada Abu Burdah, daga babansa Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi -:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu wasu abubun sha waɗanda ake yi su a can, sai ya ce: Waɗanne ne su?, ya ce: «Bit'u da Mirzu». Sai akacewa Abu Burda: Menene Bit'u? Ya ce: Tsimin zuma, Mirzu kuma: Tsimin sha'ir (karamar shinkafa), sai ya ce: «Duk abin da yake sa maye haramun ne» Bukhari ne ya fitar da shi.
-
Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu kayan shaye-shaye waɗanda ake yin su a can, shin su haramun ne, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da su. Sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Shi ne Bit'u: Tsimin zuma, da Mirzu: Tsimin shinkafa. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi: «Duk abin da yake sa maye haramun ne».