عَنْ أَبِي مُحَمَّدٍ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ العَاصِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى يَكُونَ هَوَاهُ تَبَعًا لِمَا جِئْتُ بِهِ».
[قال النووي: حديث صحيح] - [رويناه في كتاب الحجة بإسناد صحيح] - [الأربعون النووية: 41]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ibnu Amr ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi».
-
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ba ya zama mumini mai cikakken imani na wajibi har sai soyayyarsa ta zama mai bi ga abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na umarni da hani da wasunsu, sai ya so abin da ya yi umarni da shi, ya kuma ƙi abin da ya yi hani daga gare shi .