عَنْ أَبِي هُرَيْرَة رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إنَّ اللَّهَ تَعَالَى قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقْد آذَنْتُهُ بِالحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إلَيَّ عَبْدِي بِشَيْءٍ أَحَبَّ إلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وما يَزَالُ عَبْدِي يَتَقَرَّبُ إلَيَّ بِالنَّوَافِلِ حَتَّى أُحِبَّهُ، فَإِذَا أَحْبَبْتُهُ كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطِشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي بِهَا، وَإِنْ سَأَلَنِي لَأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنْ اسْتَعَاذَنِي لَأُعِيذَنَّهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [الأربعون النووية: 38]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sanar da shi yaƙi, kuma bawa Na bai nemi kusanci gareni da wani abu mafi soyuwa gareNi ba daga abin da na wajabata masa, kuma bawaNa ba zai gushe ba yana neman kusanci daNi ba har sai na so shi, idan Na so shi sai in zama jinsa wanda yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damƙa da shi, da ƙafarsa wacce yake tafiya da ita, idan ya rokeNi lallai zan ba shi, idan ya nemi tsariNa lallai zan tsare shi ».
-
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari a cikin hadisi Ƙudusi cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Duk wanda ya cutar da wani waliyyi daga cikin waliyyaiNa ya fusatar da shi ya ƙishi to haƙiƙa na sanar da shi kuma na bayyanar da adawata gare shi. Waliyyi shi ne; Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abin dake ga bawa na imani da taƙawa rabonsa na soyayyar Allah take kasancewa gare shi, kuma musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu mafi soyuwa gare shi daga abin da ya wajabta masa na aikata ayyukan ɗa'a da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana neman kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; har sai ya samu soyayyar Allah, idan Allah Ya so shi sai Allah Ya zama mai daidaita masa waɗannan gaɓɓan guda huɗu. Zai daidaita shi a cikin jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi. Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ƙafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani ƙoƙari ba sai abin da a cikinsa akwai alheri. A tare da hakan idan ya roƙi Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roƙa, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro.