Karkasawa:
+ -

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيمَا يَرْوِي عَنْ رَبِّهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى، قَالَ:
«إنَّ اللهَ كَتَبَ الحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ، ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ، فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ إلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ إلَى أَضْعَافٍ كَثِيرَةٍ، وَإِنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ سَيِّئَةً وَاحِدَةً».

[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم في صحيحيهما بهذه الحروف] - [الأربعون النووية: 37]
المزيــد ...

Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga wurin Ubangijinsa - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, Ya ce:
«Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka, wanda ya yi niyyar (aikata) kyakkyawa bai aikatata ba; Allah zai rubuta masa kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan ya yi niyyar yinta sai ya aikatata; Allah zai rubutata a wurinSa kyakkyawa goma har zuwa ninki ɗari bakwai har zuwa ninkin ba ninkin. Idan kuma ya yi niyyar mummuna bai aikatata ba; Allah zai rubuta ta kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan kuma ya yi niyyarta sai ya aikatata; Allah zai rubutata mummuna ɗaya».

[Ingantacce ne] - [رواه البخاري ومسلم في صحيحيهما بهذه الحروف] - [الأربعون النووية - 37]

Bayani

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su:
Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan.
Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar Allah mai girma ga wannan al'ummar wajen ninka kyawawa da kuma rubutasu a wurinsa, da rashin ninka munana.
  2. Muhimmancin niyya a cikin ayyuka da kuma tasirinta.
  3. Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da saukinsa da kyutatawarsa cewa wanda ya yi nufin kyakkywa bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubutashi a matsayin kykkyawa.
  4. ____
  5. ____
  6. ____
  7. ____
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari