عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قال: قال رَسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا، وَإِنْ كَانَتْ خَصْلَةٌ مِنْهُنَّ فِيهِ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنَ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: مَنْ إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ، وإذَا خَاصَمَ فَجَرَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ».
[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 48]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Abubuwa huɗu wanda ya kasance a cikinsu to ya kasance munafiki, idan akwai wata ɗabi'a daga cikinsu a tare da shi to ya kasance yana da ɗabi'ar munafunci har sai ya barta: Wanda idan zai yi zance sai ya yi ƙarya, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan aka yi rigima da shi sai ya yi fajirci, idan aka yi yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara».
[Ingantacce ne] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية - 48]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga ɗabi'u huɗu idan sun taru a tare da musulmi to ya zama mai tsananin kama da munafukai saboda waɗannan ɗabi'un, wannan ga wanda galibi suka zama a tare da shi akwai waɗannan ɗabi'un, amma wanda suka zama kaɗan to bai shiga cikin su ba, sune:
Na farko: Idan zai yi zance sai ya yi gangancin ƙarya da rashin gaskiya a cikin zancensa.
Na biyu: Idan aka yi yarjejeniya da shi ba zai cika ba, kuma ya yaudari abokinsa.
Na uku: Idan ya yi alƙawari ba zai cika shi ba kuma sai ya saɓa shi.
Na huɗu: Idan aka yi faɗa da shi kuma ya yi rigima tare da wani sai husumarsa ta zama mai tsanani, kuma ya bauɗe daga gaskiya, ya yi dabarar a kin karbar gaskiya da ɓata ta, kuma ya faɗi ɓata da ƙarya.
Domin munafunci shi ne bayyanar da sabanin abinda aka ɓoye, wannan ma'anar samammiya ce a tare da mai waɗannan ɗabi'un, kuma munafuncinsa ya zama a cikin haƙƙin wanda ya zantar da shi, kuma ya yi masa alƙawari, ya amince masa, ya yi husuma da shi, ya yi yarjejeniya da shi cikin mutane, ba wai cewa shi munafuki ne a cikin musulunci ba sai ya bayyanar da shi alhali shi yana ɓoye kafirci, wanda ya kasance a cikinsa akwai wata ɗabi'a daga waɗannan ɗabi'un; to a cikinsa akwai siffa ta munafunci har sai ya barta.