عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
ضَحَّى النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْرَنَيْنِ، ذَبَحَهُمَا بِيَدِهِ، وَسَمَّى وَكَبَّرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ عَلَى صِفَاحِهِمَا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5565]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5565]
Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka raguna biyu wato mazan tumakai, masu fararen ƙahunhuna waɗanda baƙi ya cakuɗa da su, kuma ya ce: Da sunan Allah, Allah ne Mafi girma, kuma ya ɗora ƙafarsa akan wuyansu.