عَن أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رضي الله عنها قَالت: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ كَانَ لَهُ ذِبْحٌ يَذْبَحُهُ فَإِذَا أُهِلَّ هِلَالُ ذِي الْحِجَّةِ، فَلَا يَأْخُذَنَّ مِنْ شَعْرِهِ، وَلَا مِنْ أَظْفَارِهِ شَيْئًا حَتَّى يُضَحِّيَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1977]
المزيــد ...
Daga Ummu Salama Uwar muminai matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1977]
Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wanda ya yi nufin ya yanka abin layyarsa cewa kada ya cire wani abu daga gashin kansa ko hammatarsa ko gashin bakinsa ko waninsu ko daga faratan hannunsa ko ƙafarsa idan jinjirin watan Zul-Hijja ya bayyana har sai ya yi layya.