+ -

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما أنه سمع رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول عام الفتح وهو بمكة: «إن الله ورسوله حرم بيع الخمر والميتة والخِنزير والأصنام»، فقيل: يا رسول الله أرأيت شحوم الميتة، فإنه يُطلى بها السفن، ويُدهن بها الجلود، ويَستصبِح بها الناس؟ قال: «لا، هو حرام» ، ثم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم عند ذلك: «قاتل الله اليهود، إن الله حرم عليهم الشحوم، فأَجْمَلوه، ثم باعوه، فأكلوا ثمنه».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir ɗan Abdullah - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, yana faɗa a shekarar buɗe Makka alhali shi yana Makka:
"Lallai Allah da manzonSa - sun haramta saida giya, da mushe da alade da gumaka", sai aka ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin kitsen mushe, cewa su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma ana shafe fatu da su, kuma mutane suna fitila da su? sai ya ce: "A'a, shi haramun ne", sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a wannan lokacin: "Allah Ya la'anci Yahudawa lallai Allah yayin da Ya haramta kitsensu sai suka gyara shi, sannan suka saida shi, sai suka ci kuɗinsa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2236]

Bayani

Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda ad shi - ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa a shekarar da aka buɗe Makka, alhali shi yana Makka: Lallai Allah da ManzonSa sun haramta saida giya da mushe da alade da gumaka, sai aka ce : Ya Manzon Allah, shin ya halatta mu saida kitsen mushe? domin su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma shafe fatu da su, kuma mutane suna kunna fitilunsu da su, sai ya ce: A'a, saida su haramun ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce a wannan lokacin: Allah Ya halakar da Yahudawa kuma Ya la'ancesu; lallai Allah yayin da Ya haramta musu kitsen dabbobi sai suka narkasu, sannan suka saida mansu suka ci kuɗinsa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. AlNawawi ya ce: Mushe da giya da alade: Musulmai sun haɗu akan haramcin saida kowanne ɗaya daga cikinsu.
  2. Alƙali ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi cewa abinda cinsa da anfani da shi ba ya halatta to saida shi ba ya halatta, kuma cin kuɗinsa ba ya halatta, kamar yadda yake a cikin kitsen da aka anbata a cikin Hadisin.
  3. Ibnu Hajar ya ce: Siyaƙin mai alamtarwa ne da ƙarfin dalili akan abinda mafi yawa suka yi tawilinsa cewa abin nufi da faɗinsa: "Shi haramun ne'’, siyarwa ba anfani ba.
  4. Dukkan dabarar da za'a kai ga halatta haram da ita to ita ɓatacciya ce.
  5. Al-Nawawi ya ce: Malamai su ce: A cikin gamewar haramcin saida mushe cewa saida jikin kafiri yana haramta idan mun kashe shi, kuma kafirai suka nemi siyansa, ko bada canjinsa daga gare shi, haƙiƙa ya zo a cikin Hadisi: Cewa Naufal ɗan Abdulahi AlMakhzumi musulmai sun kashe shi ranar Khandaƙ, sai kafirai suka bada dirhami dubu goma ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga jikinsa bai karɓa ba, ya ba su shi.