عن عبد الرحمن بن أبي بكرة قال: «كتب أبي -أو كتبتُ له- إلى ابنه عبيد الله بن أبي بَكْرَةَ وَهُوَ قَاضٍ بِسِجِسْتَانَ: أَنْ لا تَحْكُمْ بَيْنَ اثْنَيْنِ وأنت غضبان، فإني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: لايحكم أحد بين اثنين وهو غضبان». وَفِي رِوَايَةٍ: «لا يَقْضِيَنَّ حَكَمٌ بين اثْنَيْنِ وهو غَضْبَانُ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Abdurrahman Dan Abi Bakrata yace:"Babana ya rubuta-ko na rubuta masa-izuwa Dansa Ubaidullah Dan Abi Bakrata shi yana Alkali a Sajistan:Kada kayi Hukunci tsakanin Mutum Biyu kana mai-fushi,domin cewa naji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:kada Daya yayi Hukunci tsakanin Mutum biyu yana mai-fushi".Acikin wata ruwayar:"Kada Mai-Hukunci ya yanke Hukunci tsakanin Mutum Biyu alhali yana mai-fushi".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Mai-Shari'a Mai-Hikima ya hana Mai-Hukunci yayi Hukunci tsakanin Mutum Biyu alhali yana Mai-Fushi:Domin cewa Fushi yana tasiri abisa Ma'aunin Mutuntakar Mutum saboda haka ba'a amince ya zalunci ko ya kuskurewa gaskiya ba cikin Halin Fushinsa:sai hakan ya kasance zalunci abisa wanda Hukuncin ya hau kansa kuma Tabewa ga wanda yayi Hukunci da Zunubi akansa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin