عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
لَعَنَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّاشِيَ وَالْمُرْتَشِيَ فِي الْحُكْمِ.

[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 1336]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci.

[Ingantacce ne] - [Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi] - [Sunan Tirmizi - 1336]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mummnar addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a kan mai ba da rashawa da mai karɓarta.
Daga hakan akwai abin da ake ba wa alƙalai don su yi zalunci a hukuncin da suke jiɓintarsa; don mai bayarwa ya kai ga manufarsa ba tare da wani haƙƙi ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ba da rashawa yana haramta, da karɓarta da yin hanya zuwa gareta, da taimako a kanta; don abin da ke cikinta na taimakekeniya a kan ƙarya (ɓarna).
  2. Rashawa tana daga manyan zunubai; domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓarta da mai ba da ita.
  3. Rashawa a shari'a (Alƙalanci) da hukunci ita ce mafi girman laifi, kuma mafi tsanani; don abin da ke cikinta na zalunci da hukunci ba tare da abin da Allah Ya saukar ba.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (59)