+ -

عَنْ أَبِي بَكْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«لَنْ يُفْلِحَ قَوْمٌ وَلَّوْا أَمْرَهُمُ امْرَأَةً».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 4425]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - cewa shi yaji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«Duk mutanen da suka jiɓinta wa mace al'amuransu ba zasu rabauta ba».

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4425]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan mutane suka jiɓintawa mace suka mallaka mata al'amuransu na alƙalanta ne, ko shugabanci mai gamewa ko ma’aikata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mata ba sa jiɓintar shugabanci ko hukunci tsakaknin mutane, da makamancin wannan na gamammen shugabanci, amma keɓantattun al'amura kamar shugabancin wani hubusi, ko kula da marayu, ko shugabancin makaranta da makamancin haka to babu laifi.
  2. Bayanin raunin mace, kuma ita bata tarayya da namiji a kan gamammen shugabanci, kuma jiɓintarta misalin hakan sababi ne na rashin rabauta.
  3. Allah Ya halicci mace, kuma Ya sanya mata ɗabi'ar da ta saɓa da ɗabi'ar namiji, kuma akwai wasu al'amuran da ba ya inganta mace ta tsayu da su; dan duba ga ɗabi'arta ta musamman, haka nan akwai wasu al'amuran da ba ya inganta namiji ya tsayu da su; dan duba da ɗabi'arsa ta musamman.
  4. Rabautar da aka kore: Shine rabo a harshen shari'a, shine samun alheran duniya da lahira, kuma baya lazaimta daga bayyanar mulki da mutane su kasance a cikin yardar Allah, wanda bai kasance a cikin yardar Allah ba, to bazai zama daga cikin masu rabauta ba, ko da ya kasance a cikin mafi kyan hali a cikin abin da yake bayyana daga al'amarin duniyarsa.
  5. A cikin wannan hadisin babu tauye mace, sai dai cewa shi fuskantarwa ne ga ikonta na fuskantarwa ingantacce wanda ya dace daita.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Yaran Tailand Asami الهولندية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin