عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا، وَخَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لِنِسَائِهِمْ».

[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 1162]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.

[Hasan ne] - [Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad] - [Sunan Tirmizi - 1162]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin mafi cikar imani a cikin mutane shi ne wanda ɗabi’unsa suka kyautata, ta hanyar sakin fuska, da bayar da abu mai kyau, da kyakkyawar magana, da barin cutarwa.
Mafi alherin muminai shi ne mafi alherinsu ga iyalansa, kamar matarsa da ‘ya'yansa mata, da ‘yan’uwansa mata, da danginsa mata, domin su ne suka fi kowa haƙƙin a kyautata musu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar kyawawan dabi’u da cewar suna cikin imani.
  2. Aiki yana cikin imani, shi kuma imani yana ƙaruwa yana raguwa.
  3. Musulunci ya darajta mace, ya kwaɗaitar a kan kyautata musu.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (63)