+ -

عن عقبة بن عامر رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«أَحَقُّ الشُّرُوطِ أَنْ تُوفُوا بِهِ مَا اسْتَحْلَلْتُمْ بِهِ الْفُرُوجَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2721]
المزيــد ...

Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2721]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa mafi cancantar sharaɗin da za a cika shi ne wanda ya kasance dalili na halatta jin daɗi da mace, su ne sharuɗɗan da suke na halal ga mace ta nema a lokacin ɗaurin aure.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajibcin cika sharuɗɗa wanda ɗayan ma’aurata ya sa, sai dai sharaɗin da ya haramta halal, ko ya halatta haram.
  2. Cika sharuɗɗan aure ya fi sauran ƙarfi, domin yana matsayin halatta farji ne.
  3. Girman matsayin aure a Musulunci ta yadda ya fi kowanne sharaɗi ƙarfin cikawa.