عَنْ إِيَاسِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي ذُبَابٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَضْرِبُوا إِمَاءَ اللَّهِ» فَجَاءَ عُمَرُ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ذَئِرْنَ النِّسَاءُ عَلَى أَزْوَاجِهِنَّ، فَرَخَّصَ فِي ضَرْبِهِنَّ، فَأَطَافَ بِآلِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقَدْ طَافَ بِآلِ مُحَمَّدٍ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، لَيْسَ أُولَئِكَ بِخِيَارِكُمْ».
[صحيح] - [رواه أبو داود وابن ماجه] - [سنن أبي داود: 2146]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Iyas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 2146]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana dukan mata, sai sarkin muminai Umar Ibnu Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo kuma ya ce: Ya Manzon Allah mata sun yi wa mazajensu tawaye kuma ɗabi'unsu sun munana. Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rangwami da dukansu dukan da ba zai sa ciwo ba idan an samu sababin yin hakan, kamar idan sun ƙi bada haƙƙin miji da kuma saɓa masa da makamancin haka. Sai wasu mata suka zo a bayansa wurin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙara akan dukan mazajensu dukan da ba zai sa rauni ba, saboda mummunan aiki da wannan rangwamen, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Waɗannan mazajen waɗanda suke dukan matansu dukan da ba zai sa rauni ba ba zaɓɓɓunku ba ne.