عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ فِي الْجَنَّةِ لَسُوقًا، يَأْتُونَهَا كُلَّ جُمُعَةٍ، فَتَهُبُّ رِيحُ الشَّمَالِ فَتَحْثُو فِي وُجُوهِهِمْ وَثِيَابِهِمْ، فَيَزْدَادُونَ حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَرْجِعُونَ إِلَى أَهْلِيهِمْ وَقَدِ ازْدَادُوا حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَقُولُ لَهُمْ أَهْلُوهُمْ: وَاللهِ لَقَدِ ازْدَدْتُمْ بَعْدَنَا حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَقُولُونَ: وَأَنْتُمْ وَاللهِ لَقَدِ ازْدَدْتُمْ بَعْدَنَا حُسْنًا وَجَمَالًا».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2833]
المزيــد ...

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a, sai iskar arewa ta taso sai ta watsu a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa. sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ado, sai iyalansu suce musu: Wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ado a bayanmu".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 2833]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wani wurin da zasu dinga taruwa a wurin, babu siye da siyarwa a cikinsa suna ɗaukar abinda suke so daga gare shi, suna zuwa wurin gwargwdan kwana bakwai, sai iskar arewa ta taso, sai ta motsa a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa, sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ƙawa, sai iyalansu su ce musu: Wallahi haƙiƙa a bayanmu kun ƙara kyau da ƙawa, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin cewa 'yan aljanna suna samun ƙaruwar kyau da ƙawa.
  2. Hadisan suna sawa mutum kwaɗayi a cikin aiki nagari wanda ake taka shi zuwa wannan gidan.
  3. An keɓanci iskar arewa da ambato ne; domin cewa ita ta kasance mafi kyan iska a wurin larabawa yayin da take zuwa da alheri da kuma ruwa.
  4. Kwaɗaitarwa akan kira zuwa ga Allah ta hanyar kwaɗaitar da aljanna da kuma ni'imarta.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (36)