عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ أَهْوَنَ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا مَنْ لَهُ نَعْلَانِ وَشِرَاكَانِ مِنْ نَارٍ، يَغْلِي مِنْهُمَا دِمَاغُهُ كَمَا يَغْلِ الْمِرْجَلُ، مَا يَرَى أَنَّ أَحَدًا أَشَدُّ مِنْهُ عَذَابًا، وَإِنَّهُ لَأَهْوَنُهُمْ عَذَابًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 213]
المزيــد ...
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 213]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba a ranar lahira wanda yake da takalma biyu da igiyoyi biyu ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa saboda zafinsu, kamar yadda tukunyar tagulla take tafarfasa, kuma ba ya ganin wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi ne mafi sauƙin azabarsu, hakan dan azabar jiki da ta rai su haɗu a kansa.