عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«إِنَّ لِلْمُؤْمِنِ فِي الْجَنَّةِ لَخَيْمَةً مِنْ لُؤْلُؤَةٍ وَاحِدَةٍ مُجَوَّفَةٍ، طُولُهَا سِتُّونَ مِيلًا، لِلْمُؤْمِنِ فِيهَا أَهْلُونَ، يَطُوفُ عَلَيْهِمِ الْمُؤْمِنُ فَلَا يَرَى بَعْضُهُمْ بَعْضًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2838]
المزيــد ...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2838]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da sashin ni'imar aljanna, kuma lallai cewa mumini a cikin aljanna yana da wata shema mai girma mai yalwar ciki, ta gwal ɗaya wacce a cikinta akwai ƙofa, faɗinta da tsawonta a cikin sama mil sittin ne, a cikin kowane ɓangare da nahiya da kusurwarta daga cikin kusurwoyin ta huɗu akwai mata, sashinsu ba ya ganin sashi, mumini zai kewayesu.