عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ فِي الْجَنَّةِ شَجَرَةً يَسِيرُ الرَّاكِبُ الْجَوَادَ الْمُضَمَّرَ السَّرِيعَ مِائَةَ عَامٍ مَا يَقْطَعُهَا».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2828]
المزيــد ...

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] - [Sahih Muslim - 2828]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin dokin da aka tanada dan tsere mai sauri a cikin gudunsa zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai tiƙe ga ƙarshen abinda ya karkace daga ressanta ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin yalwar aljanna, da girman bishiyoyinta.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (38)