عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إنَّ أدنى مَقْعَدِ أحدِكم من الجنة أن يقول له: تَمَنَّ، فيتمنَّى ويتمنَّى فيقول له: هل تمنَّيتَ؟ فيقول: نعم، فيقول له: فإن لك ما تمنَّيتَ ومثله معه».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An karbo daga Abu huraira: -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai mafi karancin Gidan dayanku a cikin Al-janna ace da shi yi guri, sai yayi Guri a ransa sai ya ce da shi shin kayi Gurin? sai ya ce E sai ya ce da shi: to kana da abun da kayi Gurin da kuma wani kwatankwacin sa"
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Mafi Qarancin Mulkin Xan Al-janna da kuma darajar Masauki shi ne wanda zai samu baki xayan Burinsa, ta yadda babu wani buri da zai rage face sai ganshi, inda Allah zai ce da shi: "Kayi Buri" sai yayi burin duk abunda ya so, har sai yayi baki xayan Burikansa, Allah SWT ya ce da shi: "To lallai kana da abunda kai buri da kuma kwatankwacinsa tare da shi" qari da kuma falala da girmamawa daga Allah SWT

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Kurdawa Yaran Tamili
Manufofin Fassarorin