عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى يَقُولُ لِأَهْلِ الجَنَّةِ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ؟ فَيَقُولُونَ: لَبَّيْكَ رَبَّنَا وَسَعْدَيْكَ، فَيَقُولُ: هَلْ رَضِيتُمْ؟ فَيَقُولُونَ: وَمَا لَنَا لاَ نَرْضَى وَقَدْ أَعْطَيْتَنَا مَا لَمْ تُعْطِ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ؟ فَيَقُولُ: أَنَا أُعْطِيكُمْ أَفْضَلَ مِنْ ذَلِكَ، قَالُوا: يَا رَبِّ، وَأَيُّ شَيْءٍ أَفْضَلُ مِنْ ذَلِكَ؟ فَيَقُولُ: أُحِلُّ عَلَيْكُمْ رِضْوَانِي، فَلاَ أَسْخَطُ عَلَيْكُمْ بَعْدَهُ أَبَدًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6549]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba? Sai Ya ce: Ni zan baku mafifici daga hakan, sai su ce: Ya Ubangiji, wane abu ne maffifici daga hakan? Sai Ya ce: Zan saukar muku da yardata, ba zan yi fushi daku ba a bayansa har abada".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6549]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - zai cewa 'yan aljanna alhali su suna cikinta: Yaku 'yan aljanna, sai su amsa maSa suna masu cewa: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, Sai Ya ce musu: Shin kun yarda? sai su ce: Eh mun yarda; Danme ba zamu yardaba alhali ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarka ba! Tsarki ya tabbatar maSa Zaice: Shin ba zan baku mafifici daga hakan ba? Sai su ce: Wane abu ne mafifici daga hakan?! Sai ya ce: Zan saukar muku dawwamammiyar yarda ta; ba zan yi fushi daku a abayanta ba har abada.