عَنْ صُهَيْبٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا دَخَلَ أَهْلُ الْجَنَّةِ الْجَنَّةَ، قَالَ: يَقُولُ اللهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: تُرِيدُونَ شَيْئًا أَزِيدُكُمْ؟ فَيَقُولُونَ: أَلَمْ تُبَيِّضْ وُجُوهَنَا؟ أَلَمْ تُدْخِلْنَا الْجَنَّةَ، وَتُنَجِّنَا مِنَ النَّارِ؟ قَالَ: فَيَكْشِفُ الْحِجَابَ، فَمَا أُعْطُوا شَيْئًا أَحَبَّ إِلَيْهِمْ مِنَ النَّظَرِ إِلَى رَبِّهِمْ عَزَّ وَجَلَّ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 181]
المزيــد ...
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi? sai su ce: Ba Ka haskaka fusokinmu ba? kuma ba Ka shigar da mu aljannah ba, kuma Ka tseratar da mu daga wuta? ya ce: Sai a yaye hijabi, ba'a basu wani abu mafi soyuwa a gare su ba daga duba zuwa Ubanginsu - Mai girma da ɗaukaka -".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 181]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - zai ce musu:
Shin kuna son wani abu da zan ƙaro muku?
Sai 'yan aljanna gaba ɗayansu su ce: Shin baKa hasakaka fuskokinmu ba? Shin baKa shigar da mu aljanna ba, kuma Ka tseratar damu daga wuta?
Sai Allah Ya gusar da shamaki kuma Ya ɗauke shi; hijabinSa (shi ne) haske, ba'a basu wani abuba mafi soyuwa garesu daga duba zuwa Ubangijinsu - Mai girma da ɗaukaka ba.