عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«قَالَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَعْدَدْتُ لِعِبَادِي الصَّالِحِينَ، مَا لاَ عَيْنٌ رَأَتْ، وَلاَ أُذُنٌ سَمِعَتْ، وَلاَ خَطَرَ عَلَى قَلْبِ بَشَرٍ» قَالَ أَبُو هُرَيْرَةَ: اقْرَؤُوا إِنْ شِئْتُمْ: {فَلاَ تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ} [السجدة: 17].
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4779]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4779]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari dan girmamawa a cikin aljanna abinda wani ido bai taɓa ganin zatinsa ba, kuma wani kunne bai taɓa jin siffarsa ba, kuma haƙiƙaninsa bai taɓa afkuwa ko wucewa akan zuciyar wani ɗan Adam ba. Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Idan kun so ku karanta:
{Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki (da shi)} [al-Sajda: 17].