عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ الْجَنَّةَ، فَقَالَ: «تَقْوَى اللهِ وَحُسْنُ الْخُلُقِ»، وَسُئِلَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ النَّارَ فَقَالَ: «الْفَمُ وَالْفَرْجُ».

[حسن صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 2004]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".

[Hasan ne kuma Ingantacce] - [Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi] - [Sunan Tirmizi - 2004]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune:
Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u.
Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa.
Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta.
Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne:
Harshe da farji.
yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu.
Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Shiga aljanna yana da sabubban da suka rataya da Allah - Maɗaukakin sarki, daga cikinsu akwai: Tsoronsa, da kuma sabubban da suke rataya da mutane, daga cikinsu akwai: Kyawawan ɗabi'u.
  2. Hatsarin harshe ga mai shi, kuma yana daga sabubban shiga wuta.
  3. Hatsarin sha'awe-sha'awe da ayyukan alfasha ga mutum, kuma suna daga mafi yawan sabubban shiga wuta.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)