+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«يَا أَبَا سَعِيدٍ، مَنْ رَضِيَ بِاللهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا، وَجَبَتْ لَهُ الْجَنَّةُ»، فَعَجِبَ لَهَا أَبُو سَعِيدٍ، فَقَالَ: أَعِدْهَا عَلَيَّ يَا رَسُولَ اللهِ، فَفَعَلَ، ثُمَّ قَالَ: «وَأُخْرَى يُرْفَعُ بِهَا الْعَبْدُ مِائَةَ دَرَجَةٍ فِي الْجَنَّةِ، مَا بَيْنَ كُلِّ دَرَجَتَيْنِ كَمَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ»، قَالَ: وَمَا هِيَ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ، الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1884]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1884]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bawa Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - labarin cewa wanda ya yi imani da Allah kuma ya yarda da Shi a matsayin Ubangiji abin bauta kuma shugaba kuma mai umarni, kuma da Musulunci a matsayin Addini dan jawuwa da miƙa wuya da dukkanin umarce-umarcensa da hane-hanensa, da kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da dukkan abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi; to aljanna ta tabbata gareshi, sai Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki ga (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaita mini ita ya Manzon Allah, sai ya aikata, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kuma ina da wata dabi'ar daban wacce Allah Yake daukaka darajar bawa da ita sau dari a cikin aljanna, tsakanin kowace darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa ne, Abu Sa'ida ya ce: Waccece ya Manzon Allah? ya ce: Jihadi a tafarkin Allah, jihhadi a tafarkin Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Daga abubuwan da suke tabbatar da shiga aljanna yarda da Allah da kuma Musulunci a matsayin Addini da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi.
  2. Girmama al'amarin jihadi a tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Ɗaukaka matsayin yaƙi a cikin aljanna.
  4. Akwai wasu darajoji a cikin aljanna ba sa ƙirguwa, da matsayin da ba za su ƙirgu ba, kuma mayaƙa suna da darajoji ɗari daga cikinsu.
  5. Soyayyar sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sanin alheri, da ƙofofinsa da kuma sabubbansa.