عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: بَلَغَ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم عَنْ أَصْحَابِهِ شَيْءٌ، فَخَطَبَ فَقَالَ:
«عُرِضَتْ عَلَيَّ الْجَنَّةُ وَالنَّارُ فَلَمْ أَرَ كَالْيَوْمِ فِي الْخَيْرِ وَالشَّرِّ، وَلَوْ تَعْلَمُونَ مَا أَعْلَمُ لَضَحِكْتُمْ قَلِيلًا وَلَبَكَيْتُمْ كَثِيرًا» قَالَ: فَمَا أَتَى عَلَى أَصْحَابِ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَوْمٌ أَشَدُّ مِنْهُ، قَالَ: غَطَّوْا رُءُوسَهُمْ وَلَهُمْ خَنِينٌ، قَالَ: فَقَامَ عُمَرُ فَقَالَ: رَضِينَا بِاللهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا، قَالَ: فَقَامَ ذَاكَ الرَّجُلُ فَقَالَ: مَنْ أَبِي؟ قَالَ: «أَبُوكَ فُلَانٌ»، فَنَزَلَتْ: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَسْأَلُوا عَنْ أَشْيَاءَ إِنْ تُبْدَ لَكُمْ تَسُؤْكُمْ} [المائدة: 101].
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2359]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, sai ya yi huɗuba ya ce:
"An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa" ya ce: Babu wani yini da ya taɓa zowa sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi tsanani kamar wannan yinin, ya ce:
Sai suka rufe kawunansu suna ruri, ya ce: Sai Umar ya miƙe sai ya ce: Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi, ya ce: Sai wani mutum ya miƙe sai ya ce: Waye babana? ya ce: "Babanka shi ne wane", sai wannan ayar ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku tambayi wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}.
[al-Ma'ida: 101].
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2359]
Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, cewa su sun yawaita masa tambaya, sai ya yi fushi ya yi huɗuba sai ya ce: An bijiron da aljanna da wuta; ban taɓa ganin mafi alheri a cikin aljanna daga abinda na gan shi a yau ba.
Haka (bantaɓa ganin) mafi sharri mafi yawa daga abinda na gan shi a cikin wuta a yau ba, da kun ga abinda na gani, kuma kun san abinda na sani daga abinda na gan shi a yau da kafin yau da kun ji tsoro, tsoro mai yawa, da dariyarku ta ƙaranta, kuma kukanku ya yawaita. Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani yini bai taɓa zo wa sahabbansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - mafi tsanani daga wannan yinin ba, sai suka rufe kawunansu alhali gunji na kuka yana fita daga hanci saboda tsananin kuka. Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya miƙe sai ya ce: "Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi". Ya ce: Sai wancan mutumin ya miƙe, sai ya ce: Waye babana?
Ya ce: "Babanka shi ne wane". sai (aya) ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Maa'ida: 101].