عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما «أنَّ عمر بن الخَطَاب رضي الله عنه جاء يَومَ الخَندَقِ بَعدَ مَا غَرَبَت الشَّمسُ فَجَعَل يَسُبُّ كُفَّار قُرَيشٍ، وقال: يا رسول الله، مَا كِدتُّ أُصَلِّي العَصرَ حَتَّى كَادَت الشَّمسُ تَغرُبُ، فَقَال النَبِيُّ صلى الله عليه وسلم : والله مَا صَلَّيتُهَا، قال: فَقُمنَا إلَى بُطحَان، فَتَوَضَّأ للصَّلاَة، وتَوَضَأنَا لَهَا، فَصَلَّى العَصر بعد مَا غَرَبَت الشَّمسُ، ثُمَّ صَلَّى بعدَها المَغرِب».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullahi -Allah ya yarda da shi- "Cewa Umar Dan Khattab -Allah ya yarda da shi- ya zo Ranar Khadak bai rana ta fadi, sai ya fara zagin Kafiran kuraishawa, kuma ya ce: Ya Manzon Allah, Ya Manzon Allah, Banyi Sallar La'asar ba har rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya ce: "na rantse da Allah ban sallace ta ba, sai muka tashi zuwa Buthan, sai yayi Alwala don yin Sallah, Muma mukai Alwala don yin haka, sai mukai Sallah La'asar bayan rana ta fadi, sannan yai sallar Magariba bayan ta fadi"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Umar Allah ya yarda da shi y zo wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Ranar yakin Gwalalo bayan faduwar Rana yana la'antar kafiran Kuraishawa; saboda sun shagaltar da shi daga yin Sallar La'asar don bai sami yinta ba har Rana ta kusan faduwa, sai Annabi tsira da anminci ya rantse cewa shima bai yi sallar ba har yanzu -Annabi kuwa shi ne Mai gaskiya- Annabi ya yi haka ne don Umar ya sami nutsuwa game da lamarin da ya dame shi. Sannan sai ya mike ya yi alwalla Sahabbai ma suka yi alwalla, sai ya sallaci La'asar sannan ya sallaci Magariba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin