عن عمران بن حصين رضي الله عنهما قال: كانت بي بَوَاسيرُ، فسألت النبي صلى الله عليه وسلم عن الصلاة، فقال: «صَلِّ قائما، فإن لم تستطع فقاعدا، فإن لم تستطع فعلى جَنْبٍ».
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...
Daga Imran Bn HUsain -Allah ya yarda da su- ya ce: na kasance ina fama da Basir sai na tambayi Annabi SAW game da yin Sallah, sai ya ce: "Kayi Sallah a tsaye, idan ka kasa yi to kayi a zaune, to idan kuma ya gagara to kayi kana kwance"
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi]
Wanna Hadisin Maigirma yana bayanin yaddda Mara lafiyar da yake fama da Basir ko wani ciwo da zai hanashi tsayuwa ko wani Uzuri, sai Manzon Allah ya bada labarin cewa Asali tsayuwa, sai in ta gagara sai yayi sallah a zaune, sai in ya gagara yin sallar a zaune to sai yayi Sallah yana kwance