عن عبد الله بن عُمر رضي الله عنهما قال: «صحبت رسول الله صلى الله عليه وسلم فكان لا يزيد في السَّفَر على ركعتين، وأبا بكر وعُمر وعُثْمان كذلك».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda dasu- yace: "Na yi tafiya da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya kasance baya wuce raka'a biyu, haka ma Abubakar da Umar da Usman."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Abdullahi Dan Umar yana fada mana shi yayi tafiye-tafiye da Manzon Allah tsira da amincin Allah, hakanan yayi tafiye-tafiye da Abubakar da Umar da Usman Allah ya yarda dasu, kuma dukkaninsu sun kasance suna yin kasaru a sallolinsu masu raka'oi hurhudu,kuma basu yin sunnonin Rawatib a halin balaguro, ya ambaci Abubakar da Umar da Usman ne don ya nuna hukuncin baa shafe shi bayan wafatin Annabi ba yana nan tabbatace ne. Ya halarta a cika salla a halin balaguro, sai dai kasaru din ya fi; saboda fadinsa Madaukaki: {Ba laifa akanku da ku yi kasarun sallolin ku} fadin ba laifi da ayar tayi ya nuna cewa sauki ne aka bayar ba wai wajabci bane, saboda asali game da sha'anin salla shi ne a cika ta. abin da yafi ga matafiyi shi ne kar ya bar yin kasaru, saboda koyi da Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma don fita daga sabanin masu cewa yin kasaru tilas ne, kuma don kasancewar yin kasaru shi ne yafi gun malamai gaba daya.